Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarakunan Yarbawa Sun Yi Taron Samar Da Zaman Lafiya


Wasu sarakunan Yarbawa
Wasu sarakunan Yarbawa

Sarkin Ile Ife Oba Enitan Ogunwusi ya yi kira ga sarakunan al'ummar Yarbawa da su yi kokarin wanzar da zaman lafiya da hadin kai ga ilahirin mutanen dake yankunansu.

Sarkin Ile- Ife ya gargadi sarakunan kada su sa siyasa a harkokin mulki amma hakkinsu ne su samar da zaman lafiya cikin jama'arsu.

Sarakuna na da alhakin taimakawa jama'a domin su ci gaba amma kuma babu yadda za'a samu ci gaba ba tare da zaman lafiya ba in ji Sarkin.

Shi ma sarkin Ijesha na Ilesha Oba Adekunle Aromolaran ya bukaci sarakunan gargajiya su dinga yin abin da zai kare mutuncinsu da masarautunsu tare da yin jagoranci na gari ga talakawansu.

Shi ko sarkin Esa-Oke Oba Adeyemi Adediran ya ce majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Osun a cike da farin ciki da taron kuma sun godewa Allah da Ya ba su zarafin yin taron domin zai samar da hadin kai da zaman lafiya da kuma ci gaba.

Saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal domin jin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:55 0:00


.

XS
SM
MD
LG