Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarki Salman Bin Abdulaziz Na Saudiyya Ya Nad'a Dansa Mohammed Bin Salman Mukamin Yarima


Sarki Salman bin Abdulaziz Na Saudi Arabiya A Hagu, Yana Magana Da Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan,
Sarki Salman bin Abdulaziz Na Saudi Arabiya A Hagu, Yana Magana Da Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan,

Majalisar iyalan masarautar Saudiyya ta Amince da nadin Mohammed Bin Salman a matsayin Yarima

Sarki Salman na Saudiyya ya karawa dansa Mohammed Bin Salman mai shekaru 31 girma, zuwa mukamin Yarima, wanda hakan ya saka shi a matsayin wanda zai gaje shi, yayin kuma da shi dan nasa ke rike da mukamin ministan tsaron kasar da kuma jan ragamar wani shirin yi wa tattalin arzikin kasar garanbawul.
A yau Laraba aka sanar da wannan sauyi a karkashin wata doka, wacce kamfanin dillancin labarai mallakar kasar na SPA ya sanar.

Gabanin baiwa dan nasa wannan mukami, dokar ta nuna cewa Sarki Salman ya sauke Mohammed Bin Nayef, wanda shi ya kamata ya gaje shi daga mukaminsa, sannan ya kuma sauke shi daga mukamin Ministan cikin gida da yake rike da shi.

Shi dai Sarki Salman kawu ne ga Mohammed Bin Nayef da ya sauke.
Har ila yau dan nasa, Mohammed Bin Salman, wanda a da shi ne mataimakin Yariman kasar, zai kuma rike mukamin mataimakin Firai ministan Saudiyya.
Wannan sauye-sauye, ya biyo bayan amincewa da majalisar iyalan masarautar ta yi, inda 31 daga cikin mambobin majalisar suka amince da sauyin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG