Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Gombe Ya Dauki Dawainiyar Ilimin 'Ya'yan Talakawa da Marayu 1500


Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu

Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu ya dauki dawainiyar ba 'ya'yan wasu talakawa da marayu su 1500 ilimin firamari saboda tunawa da marigayi sarkin Gombe Usman Shehu Abubakar wanda ya gada

A jawabinsa sarkin Gombe Abubakar Shehu ya godewa Allah wanda ya bashi damar rungumar aikin taimakawa 'ya'yan talakawa da marayu domin su samu ilimin zamani da na addini.

Yace ya dauki matakin ne ganin akwai yara fiye da miliyan daya da basa makaranta walau saboda talaucin da iyayen ke fama dashi ko kuma su yaran marayu ne basu da masu kulawa dasu. Yace a duk fadin duniya Najeriya ce tafi yawan yaran da basa makaranta. Dalili ke nan da yake kokarin kawo tashi gudummawar domin rage adadin yaran da basa makaranta.

Wasu iyayen yaran da suka halarci bikin sun godewa sarkin da taimakonsa. Jauro Hamma daya daga cikin iyayen ya roki Allah ya sakawa sarkin da alheri. Shi ma mataimakin gwamnan jihar Gombe ya gargadi mutane su yi koyi da irin halin da sarkin ya nuna.

Wasu cikin yara 1500 da sarkin Gombe ya dauki nauyin karatunsu
Wasu cikin yara 1500 da sarkin Gombe ya dauki nauyin karatunsu

Daya daga cikin yaran da suka ci moriyar shirin sarkin tayi jawabi a madadin sauran yaran. Sun godewa sarkin tare da yin alkawari ba zasu ba sarkin kunya ba.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

XS
SM
MD
LG