Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Ilorin Ya Hana Wasan Yaran Fulani da Suka Saba Yi Lokacin Bikin Salla


Fulani makiyayi.

Sarkin Ilori Ibrahim Sule Gambari ya kira sarakunan Fulani da shugabannin matasan Fulani kada su shirya yin bikin sallar bana a fadarsa sabili da wasu dalilai da ba zasu rasa nasaba da matsalar tsaro ba da cutar Ebola.

Sarkin yayi kiran ne ta bakin shugaban matasan Fulani na kasa na kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara Alhaji Usman Adamu.

Yace yana kiran matasan Fulani da sarakuna da shugabannin Fulani dake jihar Kwara da bakin mai martaba sarkin Ilori cewa wasan salla da aka saba yi a fadarsa kowace shekara ya hana na bana. Baya son a yi kowane irin wasa lokacin salla a duk fadin jihar. Wasan ya kan jawo Fulani har ma daga kasar Ghana.

Kodayake bai bayyana dalilin da yasa ya hana wasan ba amma kowa ya san yadda kasar ke fama da matsalar tsaro inji Alhaji Usman Adamu. Bugu da kari sai ga kuma cutar ebola da gwamnati ke kokarin dakile wa da tabbatar cewa bata yadu ba.

Alhaji Usman yace suma sun yi farin ciki domin shi mai martaba shi ma Fulani ne kuma yana son al'adun Fulani amma sabili da ire-iren matsalolin da kasar ke fama dasu shi yasa ya na son a dakatar da wasan na wannan shekarar.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG