Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Japan Ya Sauka Daga Karagar Mulki

Sarkin Japan, Akihito

Yarima mai jiran gado Naruhito zai zama sabon sarki lokacin da wa’adin mulkin Akihito a hukumance zai kawo karshe a tsakar daren yau.

Sarkin Japan Akihito ya yi murabus daga gadon sarautarsa don ya mikawa babban dansa.

Yayain da yake jawabinsa na karshe daga fadarsa da ke birnin Tokyo a yau Talata, Akihito ya bayyana godiyarsa ga mutanan Japan na irin goyon bayan da suka ba shi na tsawon shekaru 30 da ya yi a matsayin sarki.

Ya ce ya ji dadi cewa ya samu damar yin aikinsa tare da cikakken goyon baya da kuma yarda daga mutanensa.

Yarima mai jiran gado Naruhito zai zama sabon sarki lokacin da wa’adin mulkin Akihito a hukumance zai kawo karshe a tsakar daren yau.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG