WASHINGTON, DC —
Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, Na biyu yayi kira a samar da wata doka da zata kauda kowane irin nau'i, na auren dole a tsakanin al’uma domin, kara kare, kima da mutuncin, auratayya da ma’aurata.
Sarkin, ya furta haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabanin, kula da gyaran dokoki, ta jihar Kano, a fadansa, karkashen jagorancin, Justice, Wada Umar Rano.
Sarkin, na Kano, yace matakin ya zama wajibi, idan akayi, la’akari da yanda auren dole ya dauki sabon salon a wannan zamani.
Sarkin, yace yanzu wasu mutane, ne ke amfani da dukiya, ko mukami ko kuma wani abun hannun su, wajen jan hakalin makwadaitan, iyaye, domin aurar masu da ‘ya’ya.