Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Sasa, Alhaji (Dakta) Haruna Mai Yasin Katsina, Ya Yi Bukin Cika Shekaru 31 Kan Karagar Mulki


Wani bikin nadin sarauta a Nijeriya

Sarkin Sasa Alhaji Dakta Haruna Mai Yasin Katsina, ya yi bikin cika shekaru 31 kan karagar mulki da bai ma wasu fitattun mutane sarauta tare da kira ga 'yan Nijeriya su zauna lafiya da juna.

A jiya Asabar Sarkin Sasa, Sardaunan Yamma Dr. Haruna Mai Yasin Katsina ya yi bikin cika shekaru 31 bisa gadon mulki tare da bai ma wasu fitattun mutane sarauta.

Daga bisani Sardaunan na Yamma ya gaya ma wakilinmu a birnin Badun Hassan Ummaru Tambuwal cewa ya yi farin ciki matuka da rana irin ta yau. Ya kuma gode ma sarakuna da sauran jama'ar da su ka ba shi goyon baya wajen tafi da al'amura.

Ya ce shi dai ba zai wasa kansa ba, saboda sauran jama'a masu lura da al'amura ya kamata su yanke hukunci. Sannan ya yi kira ga 'yan Arewacin Nijeriya mazauna kudu da su zauna lafiya da sauran al'ummomin yankin. Sauran mahalarta bukin sun tgofa albarkacin bakinsu ciki har da Shugaban Miyatti Allahi na jihar Kwari Alhaji Usuman Adamu, wanda ya ce ya yi farin cikimn ganin yadda kabilu dabm-dabam su ka taru wuri guda a wannan bukin. Shi kuwa Dan Madamin Jihohin Yamma, Alhaji Bello Garba ya yaba ne da sarautar da aka ba shi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG