Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SAUDIYA: Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 17


Sarkin Salman na Saudiya

Harin kunar bakin wake a kudancin kasar Saudiya ba aika da mutane 17 lahira

Wani kunar bakin wake da aka kai a kudancin kasa mai tsarki wato Saudiya ya rutsa da mutane 17.

Gidan talibijan mallakar gwamnatin kasar dake El-Ekhbariya ya sanarda tarwatsewar bom yau Alhamis.

Lamarin ya faru ne yayin da mutane suke salla a wani masallaci da jami'an tsaro suke yawan anfani dashi a birnin Abha.

Babu wani karin bayani daga mahukuntar kasar bayan sanarwar da gidan talibijan din ya bayar.

To saidai yadda kasar ta Saudiya take kai hari a kan 'yan Houthin Yemen da kuma hare-haren da jiragenta ke kaiwa kan ISIS a karkashin kawancen da Amurka ke yiwa jagoranci ba abun mamaki ba ne a ce wasu da suke goyon bayan ISIS ko 'yan tawayen Houthi su mayarda martani.

XS
SM
MD
LG