Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya ta yanke huldar diflomasiya da kasar Iran


Yan shiya sun kone kamanin sarkin Saudiya Salman Ibn Abdulaziz

Dangantakar diflomasiya ta tabarbare tsakanin kasar Saudiya da Iran

Kasar Saudi Arabia ta yanke huldar diplomasiyya kwana guda bayan da masu zanga zanga a birnin Tehran suka far ma ofishin jakadancinta domin nuna fushinsu bisa kashe wani fitaccen Malamin Shi’a da Saudiyan ta yi.

A wani martini da kamafanin dillancin labaran Iran na IRNA ya dauka, mataimakin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian, ya soki Saudiyya kan matakin da ta dauka na ranar Lahadi, inda ta kashe Sheikh Nimr-al-Nimr.

Sai dai a daya bangare kuma ministan ma’aikatar harkokin wajen Saudi, Abdel-al-Zubair ya ba da umurnin cewa dukkanin jamai’an dimplimasiyyan Iran da su fice daga kasar cikin sa’oi 48.

A cewar al-Jubeir, Saudiya ba za ta amince da ci gaba da kai hare-hare akan ofishin jakadancinta ba, domin hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.

An dai kashe Malamin Shi’an ne tare da wasu mutane 46 a kasar ta Saudiyya, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga kasashe duniya

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG