Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Ta Sake Bude Masallacin Ka’aba


Musulmai da dama yayin da suke addu'a a masallacin Al-Haram da ke Makkah a shekarar 2016.
Musulmai da dama yayin da suke addu'a a masallacin Al-Haram da ke Makkah a shekarar 2016.

Kasar Saudiyya ta sake bude masallatai biyu mafiya tsarki a addinin Musulunci, wato Al-Haram da ke Makkah da kuma Al-Masjid al Nabawy da ke birnin Madina.

Hakan ya biyo bayan rufe masallatan biyu domin wanke su, da kuma tsaftace su yayin da cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa.

A cewar gidan talabijin na Al-Ekhbariya, an rufe su ne a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar, ta hanyar tsaftace masallatan yadda ya kamata.

A kwanakin baya ne Saudiyyar ta dakatar da maniyyata aikin haji da umrah, ‘yan kasashen waje da kuma masu yawon bude ido daga kasashe a kalla 25 zuwa masallatan, domin hana yaduwar cutar.

A yanzu dai, mutum 5 ne aka bayyana cewa sun kamu da cutar a kasar.

Rahoton na gidan talabijin din Al-Ekhbariya, bai bayyana ko za a bar maniyyata aikin haji da umrah su ziyarci masallatan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG