Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura Kwanaki 11 Zaben Amurka Kotu Ta Bayar Da Izinin Bincikar Wasikun Hillary Clinton


Hillary Clinton
Hillary Clinton

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amura FBI ta sami izinin kotu don bincikar wasikun email din Hillary Clinton. Sai dai kuma 'yan jam'iyyar Democrat na ganin akwai muna kisar siyasa.

A yayin da hukumar Binciken manyan laifuffuka ta tarayya a nan Amurka ta samu takardar iznin kotu domin fara duba wasu wasikun email wadanda ake zaton suna da alaka da yadda Hillary Clinton tayi amfani da akwatin email na gida lokacin da take sakatariyar harkokin waje, ‘ya’yan jam’iyyar sun ce akwai wata munakisar siyasar da ta sanya aka bayyana wannan abu a daidai wannan lokacin.

Masu bincike na hukumar ta FBI sun shafe makonni da dama da sanin cewa wadannan wasikun Email da suka gano a lokacin wani bincke dabam da suke yi, suna da alaka da binciken Clinton da ake yi, amma bas u bayyana wannan abin ba sai ana saura kwanaki 11 kafin a gudanar da zabe.

A ranar Jumma’a darektan hukumar ta FBI, James Comey, ya aikewa da shugabannin majalisar dokokin Amurka wasika yana bayyana gano wadannan wasikun. Comey ya fada cikin wasikar tasa cewa ba a san ko wadannan wasikun suna da muhimmanci ba don ba a yi nazarinsu ba tukuna.

Shugaban ‘yan Democrat marasa rinjaye a majalisar dattijai, Harry Reid, ya fada jiya lahadi cewa Comey yana amfani da mukaminsa domin karkata akalar wannan zaben shugaban kasar, kuma watakila ya karya doka wajen yin hakan.

A cikin wata wasika, Reid yayi zargin cewa Comey ya ki yarda da bukatun da aka gabatar na ya saki bayanai masu zafi da sanatan yayi Imani hukumar FBI tana da su game da alakar dake tsakanin dan takarar shugaba na jam’iyyar Republican, Donald Trump, da kasar Rasha.

Tsohon atoni janar na Amurka, Eric Holder, da wasu tsoffin manyan jami’an ma’aikatar shari’ar Amurka da masu gabatar da kararraki su kusan 100 su ma sun bayyana damuwa kan wannan sanarwa da Comey ya bayar da kuma ganin cewa ana saura kwanaki kadan a gudanar da zabe ya bayar da ita.

XS
SM
MD
LG