Jami’ai a Amurka sun ce an shirya mataimakin shugaban Amurka Mike Pence zai gana da Jami’ai daga Korea ta Arewa a farkon wannan watan, amma Korea ta Arewan ta soke zaman tattaunawar ana daf da fara ta.
An shirya yin zaman tattaunawar ne a ranar 10 ga wata Fabrairu, yayin da Pence ya kai ziyara a Korea ta Kudu domin bikin bude wasannin Olympics na hunturu a PyeongChang, wanda aka fara ranar 9 ga wannan watan.
An shirya mataimakin shugaban kasar zai gana da Kim Yo Jong 'yar uwar shugaban Kim Jon Un da kuma Kim Yong Nam, wanda yake shugaban kasar na jeka na yi ka.
Wadannan jami'ai su ne suka jagoranci tawagar Korea ta Arewa a yayin bikin bude wasannin, kamar yadda jaridar Washington Post ta ce.
Facebook Forum