Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Doke Algeria Da Ci 94-76 A Gasar Kwallon Kwando Ta BAL

Karawar AS Dounes Senegal da GS Algeria a gasar BAL da ake yi a Kigali Rwanda
Karawar AS Dounes Senegal da GS Algeria a gasar BAL da ake yi a Kigali Rwanda

Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.

‘Yan wasan kwallon kwadon kasar Senegal na A.S Douanes sun lallasa takwarorinsu na Algeria G.S. Sortif Algeria da ci 94-76 a gasar zakarun kwallon Kwando ta nahiyar Afirka BAL.

Dan wasan Senegal Mamadou Lamine Diop ne ya samawar da kungiyarsa ta Senegal maki 18.

Hakazalika dan wasa Mohamed Harat ya samu maki 28.

Wannan gasa ita ce ta farko da aka fara wacce aka kaddamar a ranar Lahadi 16 ga watan Mayun, za kuma a kammala ta ne a ranar 30 ga watan na Mayu.

An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.

Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.

Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka. Ga jerin sunayen kungiyoyin da zakarun ‘yan wasansu da suka fi fice.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG