Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararren Masanin Ilimi Ali Mazrui ya Rasu Yau Litinin


Professor Ali Mazrui akizungumza katika chuo kikuu cha Fayetteville, Carolina ya Kaskazini.
Professor Ali Mazrui akizungumza katika chuo kikuu cha Fayetteville, Carolina ya Kaskazini.

Shahararren malamin nan dan kasar Kenya Ali Mazrui, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman ilimi da koyar da shi, kusan shekaru 40, ya rasu yau litinin a kasar Amurka.

Malamin jami’ar Ahmadu Bayero, sashen koyar da aikin jarida Alhaji Kabiru Danlami Lawanti, ya bada takaitaccen tarihin marigayi Ali Mazrui a wata hira da yayi da muryar Amurka.

Ya fara da cewa, marigayi Ali yayi karatu a birnin Mombasa kafin yaje jami’ar Manchester ta kasar Ingila. Ya kuma yi karatun digiri na biyu a jami’ar Columbia ta birnin New York na Amurka. Daga nana yayi digirin digirgir a jami’ar Oxford. Marigayin na daya daga cikin manya-manyan profesoshi 73 da duniya ta san da zamansu.

Dangane da gudunmowar da marigayi Ali ya bada, Malam Lawanti yace marigayin na tsaka-tsakiyar kasashen gabashi da na yammacin duniya.

Malam Kabiru Ya cigaba da cewa, Mr. Ali Mazrui bai taba goyon bayan masu akidar makisanci ko na jari hujja ba, yayi Imani cewa Afrika zata iya rayuwa ta hanyar samo ma kanta ainihin tsarin da ya dace da ita, don haka za a ce ba karamar gudunmowa ya kawo ba Afrika ta fannin mulki, da tsarin mulki, da kuma samar da adalci.

"Kamar marigayi Nelson Mandela, shima Ali Mazrui ya bada gudunmuwa ta fannin koyo da koyarwa. Marigayi Mandela ya fi maida hankali ne wajen gwagwarmayar samar da ‘yanci, don haka za a iya cewa gudunmowar marigayi Mazrui ta linka ta marigayi Mandela saboda maida hanakali da yayi wajen koyas da samun ‘yanci na din-din-din" a ta bakin Malam Kabiru.

kamar yadda za ku ji a nan, ga hirar da ma'aikaciyar muryar Amurka, Halima Djimrau tayi da Kabiru Lawanti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG