Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shan Maganin Kanjamau Da Zarar An Kamu Da Ita Na Iyaka Kashe Kaifin Kwayar Cutar Gaba Daya


Kwayar maganin HIV
Bincike na nuni da cewa, jinyar mutanen da suka kamu da cutar kanjamau da zarar an tabbatar sun kamu da kwayar cutar HIV zai iya taimakawa wajen maganin kaifin cutar.
Masu ilimin kimiyya a kasar Faransa sun yi wannan binciken ne a kan wadansu mutane 14 da suke dauke da cutar da aka fara basu maganin kashe kaifin cutar nan da nan daga baya aka daina basu, bayan shekaru bakwai aka sake gwada su aka tarar kwayar cutar bata sake yaduwa ba.
Binciken na nuni da cewa, duk da yake maganin bai warkar da cutar baki daya ba, yana kashe kaifin kwayar cutar yadda wanda yake dauke da ita zai ci gaba da rayuwa ba tare da jinya ba, duk da haka za a iya tarar da kwayar cutar a jikin mutum idan aka gwada shi.
Yawancin sama da mutane miliyan 34 dake dauke da kwayar cutar HIV a fadin duniya suna shan maganin kashe kaifin cutar da ake kira da turanci “antiretroviral therapy” duk tsawon rayuwarsu. Wannan maganin yana kuma da illa a lafiyar mutum.
Rahoton hukumar yaki da cutar HIV ta Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS) ya nuna cewa, yawan wadanda suke dauke da kwayar cutar HIV ya ragu zuwa miliyan 2,5 inda wadanda suka kamu da cutar a shekara ta dubu biyu da daya ya ragu da kashi ishirin bisa dari daga adadin wadanda suka kamu da cutar a shekara ta dubu biyu da daya. Mutane 1.7 kuma suka mutu ta dalilin cutar kasa da mutane miliyan 2.3 da suka rasu da cutar a shekara ta dubu biyu da biyar ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG