Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shan Taba Da Zarar Mutum Ya Tashi Zai Iya Sa Mutum Ya Kamu Da Cutar Sankara


Wani mutum yana kuna taba
Wani bincike da aka gudanar a wata Jami’ar Amurka ya bayyana cewa, shan taba sigari da zarar mutum ya tashi daga barci yana iya sawa ya kamu da cutar huhu ko hakori.

Masu bincike sun ce sun sami burbudin taba dake haddasa cutar sankara da ake kira NNAL a jikin wadanda suke shan taba da zarar sun tashi daga barci fiye da wadanda suke jira sai bayan minti talatin ko fi bayan sun tashi daga barci kafin su sha taba.

Binciken ya nuna cewa, yawan NNAL a jikin mai shan taba da wayewar gari yana karuwa da tsawon shekarun shan taba, kuma yana iya zama hadari ga mai shan taba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG