Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Suna Gadin Dzhokhar Tsarnaev A Asibiti Bayan Kama Shi Jiya


jami'an tsaro suna bincike Dzhokhar Tsarnaev bayan sun kama shi

Mutum na biyu da ake zargi da kai harin bom a birnin Boston Dzhokhar Tsarnaev yana kwance a wani asibiti cikin wani mawuyacin hali

An kawo karshen zaman dardar da aka yi na tsawon mako guda a birnin Boston jihar Massachusetts da kewaye bayanda jami’an tsaron Amurka suka rutsa, suka kuma kama mutum na biyu da ake zargi da kai harin boma bomai a wurin gudun ya da kanen wani da aka yi a birnin Boston.

Dzhokhar Tsarnaev dan shekaru 19 yana kwance a asibitin Beth Isreal Deoconess dake birnin Boston cikin wani yanayi mai tsanani. An kashe wansa dan shekaru 26 a wata musayar wuta da aka yi da ‘yan sanda ranar alhamis yayinda Dzhokhar ya tsere da kafa.

‘Yan sanda sun rutsa kanen Tsarnaev ne da ya boye cikin wani kwale kwale a bayan wani gida dake garin Watertown jiya jumma’a. Hukumomi sun kamashi bayan musayar wuta.

Kama mutumin na biyu ya sa mutane a garin Watertown inda aka kama shi, suka rika shewa suna murna. ‘yan kallo sun yi ta jinjinawa ‘yan sanda da jami’an hukumar binciken kwakwaf ta FBI yayinda suka shiga motocinsu suna barin Watertown.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG