Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekarun Wata Sun Kai Miliyan Dubu Hudu da Miliyan 51


Cikakken Wata

A wani bayanin da suka wallafa a cikin wata Mujallar Kimiyya, masanan sun kiyasta cewa suna jin shekarun wata a yanzu sun kai shekaru miliyan dubu 4 da milyan 51.

Haka kuma sun ce suna kyautata zaton cewa Allah Ya hallici Wata shekaru miliyan 60 bayan halittar duniyar kanta.

Cikakken wata mai shekaru miliyan dubu hudu da miliyan hamsin da daya
Cikakken wata mai shekaru miliyan dubu hudu da miliyan hamsin da daya

Kafin zuwa yanzu, kiyasin da ake shine cewa wai Wata yana da shekaru tsakanin miiyan 150 da miliyan 200 ne.

Ance masanan kimiyyar na Jami’ar U-C-L-A ta Los Angeles sun gudanarda binciken nasu ne ta hanyar nazarin duwatsun da wasu Kumbunan Apollo suka dawo da su doron duniya bayan tafiyar da suka yi zuwa kan Wata a shekarar 1971.

XS
SM
MD
LG