Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Da Yake Ikirarin Shine Shekau Ya Fito A Wani Sabon Vidiyo


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Mai ikirarin shine Shekau yace kariya sojoji suke yananan daram babu abunda ya same shi.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yau ya sake bayyana a wani fefen vidiyo da aka nuna a dandalin sada zumunta lahadin nan. Yana cewa ina cikin koshin kafiya, yana watsi da sanarwar da rundnar sojin Najeriya ta fitar cewa ta ji masa rauni.

A maganar da yayi da Hausa, da Larabci, da kuma wani harshe da ake amfani da shi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wani mutum da yayi ikirarin cewa shi ne Abubakar Shekau, yayi magana na tsawon minti 40 a vidiyon da ya maida hankali ga sojojin Najeriya, "kuna yada labarai, ni kuma ina wallafa shi a dandalin sada zumunta,cewa kun kun jikkata ni ko kun kashe ni, amma gani nan.

An saka vidiyon ne a a dandalin Youtube da kwanan watan yau 25 ga watan Satumba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG