Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shi'a: Za Mu Fito Muzaharar Ashura A Najeriya


Muhammad Ibrahim Gamawa
Muhammad Ibrahim Gamawa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fito karara ta ce duk wata zanga zangar almajiran El-Zakzaky za su dauke a matsayin aikin ta'addanci.

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya ce duk wata muzahara da almajiran El-zakzaky suka shirya za su gudanar tamkar aikin ta’addanci ne.

Adamu a sanarwa da kakakin rundunar, Frank Mba, ya fitar, ya ce rundunar na sane da shirin ‘yan Shi’a na kungiyar IMN na fitowa don gudanar da gagarumar zanga-zanga da ka iya ta da fitina a yankunan Najeriya.

Don haka rundunar za ta tunkari duk mai shirin wannan zanga-zanga a matsayin mai aikin ta’addanci don an haramta kungiyar ta almajiran El-zazzaky IMN a takaice.

Daya daga masu magana a madadin almajiran na El-zazzaky, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya ce za su fito muzahara a ranar Talatar nan don ranar Ashura da ‘yan Shi’a kan yi juyayi a duk shekara kenan.

Rundunar dai ta ‘yan sanda ta bukaci iyaye su hana ‘ya’yansu aukawa kungiyoyin ta da hankali ko zanga-zanga marar bin ka’ida.

Rahotanni na bayyana cewa almajiran El-zakzaky ka iya amfani da damar ta gagarumar zanga-zanga don tilasta gwamnati ta saki shugabansu da ake gudanar da shari’arsa a babbar kotun Kaduna.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG