Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Dole Ne Najeriya Ta Ci Bashi?


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yayinda gwamnatin shugaba Buhari ke shirin neman izinin Majalisar Dattawan kasar ta ciwo bashin dallar Amurka miliyan dubu dari biyar da rabi, kawunan ‘yan kasar ya rabu a kan wannan shirin

Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari, na neman amincewar Majalisar Dattawan kasar domin ya ciwo bashin dalar Amurka miliyan dubu dari biyar da rabi, ($5.5bn).

Sai dai wannan yunkurin ya sa wasu hukumomin kasa da kasa da jama’ar kasar jan kunnuwan shugabannin na Nigeria game da bashin. Su kansu ‘yan kasar kawunansu sun rabu akan lamarin.

Shugabannin Bankin Duniya, da Hukumar Bada Lamuni Ta Duniya ta IMF, sun gargadi Najeriya da tayi taka-tsantsan kan ciwo bashin.

Malam Sha’aibu Idris, wani kwararre akan sha’anin tattalin arziki, ya ce akwai alfanun cin bashi da kuma rashin alfanunsa. A cewarsa, basussukkan dake kan Najeriya da ta ciwo daga hanyoyi daban daban a can baya, sun yi yawa,saboda haka bai ga dalilin da kasar zata ci wani sabon bashin ba.

Amma Malam Ahmed Yusuf, tsohon babban daraktan Bankin Unity dake Abuja, ya ce cin bashin na da mahimmanci kuma zai yi tasiri saboda gwamnatin zata yi anfani da bashin ne wajen gina abubuwan da zasu taimakawa habakar tattalin arzikin kasa.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:50 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG