Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Hukumomin Zaben Jihohi Zasu Iya Gudanar da Zaben Gwamnoni da Adalci?


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.

Watanni biyu bayan zaben kananan hukumomi a jihar Yobe hukumar zaben jihar tace tana iya gudanar da zaben gwamna idan an sakarmata mara.

Hukumar zaben jihar Yobe tace tana iya gudanar da zaben gwamna mai inganci ba tare da wata matsala ba idan an bata daman yin hakan.

Alhaji Muhammed Jauro Abdu shugaban hukumar zaben jihar Yobe yace yana da kwarin gwiwa hukumomin zaben jihohi na iya gudanar da kowane zabe har da na gwamna. Yace idan aka sakar masu mara zasu iya shirya igantattun zabuka.

Shugaban hukumar yayi furucin ne a wani fira da yayi da wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu. Da ta ce masa 'yan Najeriya na ganin cewa hukumomin zaben jihohi suna cikin aljifan gwamnoni da suka nadasu sai yace shi bai yarda ba. Yace kuma komenene mutum ya fada ba zai hana korafi ba. Wani ma zai ce kafi kowa muni a duniya. Yace a saninsa tunda ya kama aikin shugabancin hukumar yau shekaru shida ke nan gwamnan jihar bai taba tsoma baki cikin aikinsu ba. Yace ko a yadda ko kada a yadda abun da ya fada shi ne gaskiyan.

Yace idan aka basu kayan aiki aka sakarmasu mara zasu yi zabe mai inganci har ma da zaben gwamna. Yace zasu aiwatar da shi fiye da yadda ake zato. Amma ya yi fatar 'yan siyasa zasu koyi rungumar kadara. Yace yakamata su gane cewa babu yadda mutane biyu zasu tsaya takara dukansu su ci. Dole daya ya fadi daya kuma ya ci. Yakamata mutane su daina korafe-korafe su karbi abun da ya faru. Idan mutum ya ci a tayashi murna. Wanda kuma ya fadi ya hakura.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG