Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ke Haddasa Tashin Farashin Kaya Gabanin Bikin Sallah?


Kasuwa
Kasuwa

Gabanin ko wane bikin sallah walau na Musulunci ko ta Kiristanci farashin kayayyaki su kan yi tashin goran zabi lamarin da malaman addini suka alakantashi da yawan son abun duniya na mutane da rashin tsoron Allah da kuma karanci kaya wani lokacin.

Tsauwala farashin kayan masarufi a kasashe masu tasowa wani abu ne dake kara ta'azzara a duk lokacin da aka dukufa da shirye-shiryen sallah watau ta Musulunci ko ta Kiristanci.

Amma a kasashen da suka ci gaba 'yan kasuwansu su kan karya farashin kaya ne. Wannan al'amari ya jawo hankulan shugabannin addini.

Uztaz Halidu Yahaya wani malamin addinin musulunci yace abun dake haddasa hakan kuwa domin komi ya koma kasuwa, ma'ana mutane kudi suka dogara a kai.Yana mai cewa duk abun da za'a yi sai kasuwa. Komi ya koma sai da kudi ba irin tarbiya ta da ba. Yanzu ta kubuce mana. Da ba abun duniya aka sa a gaba ba kamar yanzu.

Shi ma Rverend Suleiman Labbo daya daga cikin malaman addinin Kirista a Maradi ya bayyana nashi ra'ayin akan lamarin. Yana mai cewa a kasashen Afirka inda ake da karancin tattalin arziki mutane suna son su yi arziki cikin gaggawa ba tare da sai sun wahala sosai ba. Yace dalili kenan wadansu dake hanzarin samun kudi idan sun samu hanyar samu daga wasu zasu yi kokari su kawo wata hujja ta samun kudin daga garesu. Shi ya sa 'yan kasuwa ke anfani da bukukuwan sallah su labtawa kayansu farashi domin su ci kazamar riba.

Amma 'yan kasuwa na ganin akwai wani dalili daban. Alhaji Sani Shekarau Garo shugaban 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga ketare na cewa wani lokacin suna samun karin farashin kaya daga masu sarafasu.

Sai dai malamai sun yi gargadi akan illolin dake biyo bayan farashin kayayyaki da nufin cin kazamar riba.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG