Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Sa Wasu Kasashen Larabawa Suka Yanke Huldar Diflomasiya da Qatar


Shugaban Amurka Donald Trump da Sarkin Saudiya Salman yayin ziyararsa zuwa kasashen Larabawa
Shugaban Amurka Donald Trump da Sarkin Saudiya Salman yayin ziyararsa zuwa kasashen Larabawa

A ra'ayin wasu masana kasashen da suka yanke huldar diflomasiya da kasar Qatar sun yi hakan ne domin su farantawa kasashen turai rai saboda ita Qatar kasas ce da bata sayen komi basshi daga kowace kasa a duniya kuma bata karbar bashi, tana kuma biyan bukatun 'yan kasarta ta duk hanyoyin rayuwa.

A jiya Litinin ne ma ,kasashen Saudiya da Masar da Baharain da kuma Daular Larabawa suka sanar da katse huldar diplomasiyyarsu da kasar Qatar a bisa zarginta da tallafawa ayyukan ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Al-Qaida da ISIS da Kungiyar 'Yan uwa Musulmi kana kuma da ma yin katsalandan a cikn harkokin cikin gidansu.

Baya ga wannan ma an kori kasar ta Qatar daga rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiya ke jagoranta a yakin kasar Yemen.

Wannan dambarwa a fagen diplomasiyyar kasashen na Larabawa na zuwa ne a kasa da kwanaki 15 bayan ziyarar da Shugaban Amurka Trump ya kai Saudiya inda ya bukaci kasashen Musulmi da su dauki kwararan matakai wajen yaki da kaifin kishin Islama.

To sai dai kuma masana tattalin arziki da diflomasiya irinsu Abdullahi Prembe na ganin akwai lauje cikin nadi.

Masanin dai na ganin wannan janyewar ka iya shafan ita kanta kasar Qatar ganin cewa ko a baya akwai wasu kasashe da suka fuskanci takunkumi.

Ya zuwa yanzu tuni Qatar din ta musanta zargin marawa 'yan ta'addan baya da suka hada da kungiyar ISIS, inda ta ce matakin ' ba shi da tushe' .kuma tuni aka dakatar da jiragen saman kasar Qatar bi ta sararin samaniyar kasashen Masar da Saudiya, yayinda aka cigaba da takun sakar dake barazana ga manayn harkokin sufurin sama.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG