Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ya Ya Za Ta Kaya a Babban Taron PDP?


Hedkwatar Jam'iyar PDP da ke Abuja a Najeriya
Hedkwatar Jam'iyar PDP da ke Abuja a Najeriya

Akwai alamu da ke nuna cewa, mai yiwuwa akai ruwa rana a babban taron da jam'iyar PDP mai adawa ke yi a Abuja, bayan da gwamnonin kudu maso kudu suka nuna alamun goyon bayan dan takarar da ya fito daga yankinsu a matsayin dan takarar shugaban jam'iyar.

Babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya na gudanar da babban taronta a Abuja, babban birnin kasar.

Taron zai mai da hankali ne wajen zaben shugabannin da za su ja ragamar tafiyar da al’amuran jam’iyar na wasu shekaru masu zuwa.

Mukamin kuma da ya fi jan hankali shi ne na shugaban jam'iyar.

Wannan babban taro shi ne na farko tun bayan da jam’iyar ta sha kaye a hannun jam’iyar mai mulki ta APC a shekarar 2015.

Tun gabanin taron alamu sun nuna gwamnonin jam’iyar, musamman gwamna jihar Rivers, Ezenwo Nyesom Wike na mara baya ga dan takarar shugabancin jam’iyar Uche Secondus.

Hakan ya sa wasu daga kudu maso yammacin kasar suke ganin hakan zai iya shafar sabon hadin kan jam’iyar.

Shi dai Secondus ya fito ne daga kudu maso kudancin Najeriya.

Masu lura da al'amura na ganin wannan taron zai zamanto tamkar zakaran gwajin dafi ne ga sabon hadin kan da jam'iyar ta samu.

Tuni dai Bode George, ya bayyana cewa ba za a yi “wannan kwamacalar da shi ba.”

Ya kuma janye takararsa, inda ya ce ya kamata gwamna Wike ya bai wa Yarbawa hakuri, yana mai cewa ya ci musu zarafi.

Bayani sun yi nuni da cewa sakamakon taron zai iya kai har zuwa dare kafin a same shi.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin samun cikakken bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG