Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Bikin Kirsimati da Hauhawar Farashin Kaya a Adamawa


Yayinda mutane ke murna da zagayowar bikin Kirsimati saboda zaman lafiya da aka samu sabanin yanayin shekarun da suka gabata, tashin gwauron zabi da farashin kaya suka yi, musamman kayan gwari, ya sa jama'a na korafi

A jihar Adamawa an soma kawata birane domin bikin Kirsimati da na sabuwar shekara mako daya bayan Kirsimatin.

Mabiya addinin Kirista na garzayawa kasuwa domin sayen kayan sallah inda wata mai suna Esther Musa ta bayyana farin cikinta ganin yadda mutane ke hada-hada sabanin shekarun da suka wuce. Injita, duk da tsadar kaya mutane suna saye cikin walwala.

A cewar wasu, kowace shekara idan wani biki ya karato kaya sukan yi tsada. Ba sabon abu ba ne. Haka ke faruwa kowace shekara lamarin da wasu suka kwatantashi da rashin yi masu adalci.

Sai dai 'yan kasuwa na da nasu ra'ayin daban. Yayin da wasu suke yiwa Allah godiya da ganin zagayowar bikin cikin koshin lafiya, wasu kuma sun dora alhakin tashin farashin kayan ne akan wasu dalilai daban. Wuraren da suke sayo kayan gwari kamar Zaria akan kara masu farashi a daidai wannan lokacin. Masu motoci ma suna kara kudi musamman ma idan an samu karancin man fetur. Fataken dake zuwa sayo kaya na raguwa a wannan lokcin abun da dake rage yawan kayan a kasuwa amma kuma lokacin ne ake samun karin jama'a masu zuwa saye..

Wani Shugaban 'yan kasuwa Lawal Auta ya jaddada karancin kayan da jawan masu saye a matsayin dalilin da ya sa farashi ke tashi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG