Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Nishadi Tare Da Musa Mai Sana’a


Musa Mai Sana’a Jarumin Fina Finai
Musa Mai Sana’a Jarumin Fina Finai

Shirin Nishadi yau ya sami zantawa Musa Mai Sana’a, jarumi kuma mai shirya fina finai wanda ya shafe shekaru yana wannan sana’a.

Musa Mai Sana’a dai ya taso tun yana Yaro lokacin ya na makaranta idan za’a yi wasan dabe ana saka shi ciki, duk da yake mutum ne mai son jama’a da wasa da dariya. Ya kuma fada mana cewa yana kallon wasan Boloko tun yana yaro wanda hakan ne ya janyo hankalinsa da saka masa sha’awa ga wannan sana’a.

Duk da cewa yafi fitowa a bin raha a cikin fina finan sa, amma komai yazo masa to zai mai da hankalinsa domin tabbatar da cewa yayi abin kirki.

Game da masana’antar Kannywood kuwa Musa dai yace an sami ci gaban mai hakar rijiya, domin an kasa cin ma nasarar abinda aka fuskanta, sakamakon rashin hadin kai duk kuwa da cewa akwai kungiya amma bata tsaya da kafafunta ba tukunna.

Saurari hirar Musa Mai Sana’a.

XS
SM
MD
LG