Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shiyyar Sakkwato Ta PDP Ta Musanta Zargin Ramuwar Gayya


 Gwamna Aminu Waziri Tambuwal
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

'Yan makwanni bayan ayyana Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya sake cin zaben gwamnan jahar Sakkwato, jam'iyyar APC ta fara kuruwar cewa an fara ma 'ya'yanta bita da kulli.

Babbar jam’iyyar adawa a Sakkwato, APC, ta zargi jam’iyya mai mulki da huce haushin cin zabe da kyar kan wasu ma’aikatan gwamnatin jahar. APC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa wannan lamari na uzzura wa ma’aikatan gwamnati da ake zargin sun goyi bayan jam’iyyar ta APC a zaben da ya gabata, ya fi Kamari a wasu manyan ma’aikatun gwamnati, da kuma kananan hukumomi. Abin bai tsaya ga ma’aikatan gwamnati ba, ya zarce har ya zuwa ‘yan kasuwa da ma daidaikun jama’a ta hanyoyi daban-daban.

Shugaban jam’iyyar APC din na jahar Sakkwato, Isah Sadiq Achida, ya kuma yi jawabi ga wani taron manema labarai domin kokawa akan lamarin. Ya ce wannan bi ta da kullin siyasa ya hada da rike albashi da sauya wuraren aiki ko kuma cire su daga irin aikin da su ke yi ba tare da ba su wani aikin na dabam ba, duk da zummar dai a kuntata masu, saboda zargin sun goyi bayan APC a zaben da ya gabata.

Alhaji Achida ya ce, “ Abubuwan sun kai har inda aka hana talakawa diban ruwa a rijiyoyin da aka gina da kudaden al’umma; an hana wasu ‘yan kasuwa su baje haja a kasuwanni, an kuma kwace ma wasu shuguna ba don sun aikata wani laifi ba, ba don rashin biyan haraji ba.”

To sai dai bangaren gwamnatin jahar ya musanta akasarin zarge-zargen, duk da yake, a ta bakin wani tsohon dan majalisar dokoki kuma mashawarci na musamman ga gwamna, Bello Malami Tambuwal, aikin gwamnati ya na iya kai mutum a ko ina. Ya ce duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati sabbin shugabannin kan nada wasu amintattu da za su taimaka masu. Ya ce dama shi aikin gwamnati ya gaji haka. Hasali ma, in ji Malami, akwai wasu bayanannun ‘yan APC din da har yanzu su na daiki tare da gwamna.

Ga Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG