Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shoprite Zai Rufe Wani Kantinsa a Kenya


Shagon Shoprite da ke Abuja

Katafaren kantin nan na Shoprite mallakar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa zai sallami ma'aikata 115 sakamakon rufe kantinsa na Kenya da zai yi.

Shoprite ya bayyana wannan matakin ne a cikin wata wasikar da ya aikewa kungiyar kwadago ta kasar Kenya.

"Za mu rufe shagonmu na City Mall da ke garin Nyali a birnin Mombasa, kafin karshen wannan watan da müke ciki," in ji kantin.

Hakan dai na faruwa ne kasa da shekara daya bayan da aka bude shagon na Shoprite a Mombasa.

A ranar Litinin din da ta gabata Shoprite ya dauki wani mataki makamancin wannan a Najeriya inda ya bayyana yana nazarin rufe dukannin shagunansa da ke kasar Najeriya.

Lamarin da bai yi wa 'yan kasar dadi ba sakamakon yadda ake fargabar mutane za su rasa ayyukan yi sannan wuri ne da jama'a ke zuwa a lokutan bukukuwan sallah da na kirsimeti.

Shoprite ya alakanta wannan matakin da yake ta dauka da yanayin yadda kantunan nasa da ke kasashen waje suke kawo musu ci gaba ko koma baya.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG