Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Bukaci A Daina Goyon Bayan Mayakan M23


Yan Tawayen M23
Yan Tawayen M23
Shugaba Barack Obama na Amurka ya jaddadawa shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda irin muhimmancin dake tattare da “kawo karshen bayarda dukkan goyon baya” ga ‘yan tawaye a kasar Kwanbgo ta Kinshasa makwabciyarsa.

Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Rwanda da Uganda cewar su na goyon bayan kungiyar ‘yan tawaye ta M23, wadda kwanakin baya ta janye daga garin Goma na gabashin kasar Kwango bayan da ta kwace shi. Kasashen biyu sun musanta wannan zargi.

Fadar White House ta ce jiya talata, Mr. Obama yayi magana da Mr. Kagame ta wayar tarho, inda yayi kira a gare shi da ya cika alkawuran da yayi a tarurrukan neman zaman lafiya a yankin domin a samu cimma yarjejeniyar siyasa da zata hada da kawo karshen cin kare babu babbaka na kwamandojin M23 wadanda suka keta hakkokin bil Adama.
Yace ya kamata a kawo karshen wannan rikici tare da yarjejeniyar da zata mutunta diyaucin kasar Kwango ta Kinshasa, da takalar tsaron yanki da kuma batutuwan tattalin arziki da na mulki.
XS
SM
MD
LG