Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Ba Da Umurni a Rabawa Jihohi Biliyan 500


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ba ministar kudi da gwamnan babban bankin kasar umurnin sakarwa jihohi Naira biliyan 500 cikin gaggawa.

Shugaban ya ce kudaden na cikin rarar da aka samo daga kungiyar Paris Club da ta mayarwa Najeriya saboda ta biya fiye da bashin da kungiyar ke binta.

To sai dai yayin da ake shirin raba masu kudaden akwai wasu sama da Naira biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka ba su na yadda za su yi amfani da kason farko.

Sabanin haka sun yi abun da suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.

A yanzu shugaban na fatan za'a bi ka'ida a wannan karon, inda ya yi a garesu da su yi abin da ya kamata.

Domin jin karin bayani kan wannan batu, saurari abin da kakakin shugaban kasan Malam Garba Shehu ya ce a wannan rahoto da Umar Faruk Musa ya hada.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG