Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari ya bada umurnin bincikar wata sabuwar badakalar sayen kayan yaki


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Gwamnatin Buhari ta bankado wata badakalar sayen kayan yaki wa sojojin sama wadda zata mayar da zargin da ake yiwa Sambo Dasuki tare da wasu tamkar wasan yara

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umurni ga hukumar dake binciken cin hanci da rashawa ta EFCC ta gudanar da cikakken bincike akan tsohon hafsan hafsoshin soji da tsohon hafsan sojin sama da wasu manyan sojoji su 17 tare da tsohon mai ba tsohon shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki akan zargin wata sabuwar badakalar,

Wannan sabuwar badakalar da ajka bankado ta faru ne a faggen sayo makamai da jiragen sama da sauran wasu ayyukan tsaro da suka wakana tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015.

Yanzu an gano cewa anakashe nera miliyan dubu ashirin da tara da dalar Amurka miliyan dubu biyu wurin sayo kayan yaki ma sojojin sama kawai kafin ma a je manya manyan bangarorin sojojin Najeriya kamar yadda bincike ya bayyana.

Banda hafsoshin sojojin masu aiki da wadanda suka yi titaya da za'a bincika akwai wasu kamfanoni guda ashirin da daya wadanda za'a gudanar da bincike a kansu domin dasu aka yi anfani wurin gudanar da badakalar. Ana ma kyautata zaton kamfanonin na wasu da ake zargin ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG