Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari ya bukaci 'yan kasuwa da su taimaka


Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da sakataren harkokin waje Amirka John Kerry
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da sakataren harkokin waje Amirka John Kerry

Shugaba Muamadu Buhari ya bukaci yan kasuwa da su taimaka wajen habaka tattalin arzikin Nigeria

A wani jawabin daya gabatar, shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria yace kodayake ya san hakkin daya rataya akan gwamnatinsa wajen samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci dana tattalin arziki, dole ne 'yan kasuwa su taimaka da daukan nauyin habaka tattalin arziki da inganta kasuwanci a matsayin kokarin samun ci gaba.

Shugaban na Nigeria yace ya zama wajibi, gwamnati da 'yan kasuwa su tashi tsaye yayinda ake kokarin karkata harkokin tattalin arziki daga dogoro akan man fetur zuwa wasu farnoni.

Yace musaman Nigeria zata yi maraba da wadanda suke son zuba jarurruka a Nigerian a aiyukan hako ma'adinai. Yace zai yi iyakacin kokarinsa wajen samar da aiyukan yi domin cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

Shugaba Buhari yace babu wata hanyar yin haka illa habaka harkokin masana'antu da gine gine da kuma kafa kamfanoni. Ya kuma sake jadadda kudurin Nigeria na hada hannu da 'yan kasuwa domin cimma muradu fadada tattalin arziki.

Yace akwai albarkatu da yawa a Nigeria in baicin mai, a saboda haka gwamnatinsa zata maida hankali akan sauran albarkatu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00

XS
SM
MD
LG