Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnonin Jihohin Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Gwamnonin jihohin Najeriya sun gana da shugaban kasa Muhammad Buhari inda suka tayashi murna da dawowa lafiya da kuma irin taimakon da ya yi masu wajen biyan albashi da tallafawa tattalin arzikin jihohinsu

Yau shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana da gwamnonin jihohin Najeriya.

Gwamnonin sun kawo masa ziyarar fatan alheri ne tare da yi masa murnar samun koshin lafiya.

Sun yi anfani da ziyarar sun yi masa godiya ta musamman akan dokin da ya basu wanda ya fitar dasu daga kasa biyan albashi da alawus da kuma samar da hanyoyin bunkasa noma domin inganta rayuwar al'umma.

Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, shugaban kungiyar gwamnonin yace babban makasudin ziyararsu shi ne su yiwa shugaban barka da zuwa tare da yi masa godiya. Sun kara tabbatar wa shugaban suna tare kuma zasu taimaka ta kowace hanya.

Akan cewa duk da taimakon da shugaban kasa ya ba jihohin wasunsu har yanzu basu biya albashi ba. Gwamna Yari ya ta'allaka hakan da raguwar kason da suke samu daga gwamnatin tarayya da faduwar Nera.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:07 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG