Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari ya kaddamar da binciken kwakwaf kan kasafin kudi


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Bisa ga abubuwan da suka faru bayan da shugaba Buhari ya mikawa majalisar kasa kasafin kudin bana ya sa shugaban ya kaddamar da binciken kwakwaf kan kasafin da majalisa ta maido mashi.

Shugaba Buhari da mataimakinsa Farfasa Yemi Osinbajo sun dukufa wajen yiwa kasafin kudin da majalisa ta maido masu binciken kwakwaf.

Duba kasafin kudin shafi shafi wani sauyin salo ne da ba'a saba gani a kasar ba. Shugaban na yanzu yana takatsantsan da lamarin kudi domin muradun yaki da zarmiya da aka saba yi can baya.

Kwamred Abubakar Abdulsalam dan rajin yaki da cin hanci da rashawa ya yadda da matakin da shugaba Buhari ya dauka na tabbatar cewa ba'a yi mashi coge ba. Yace hanzari bai taba haifar abu mai kyau ba. Yace a yi la'akari da lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin. Cikin kwanaki biyu aka ce kasafin ya bata. Daga baya kuma aka ce an samu wani.wanda aka ce yana kunshe da abubuwan da basa cikin na farko.

Abubakar Abdulsalam yace duk mutumin da yake da hankali dole ne ya zauna ya sake dubawa ko abun da ya mika aka mayar masa dashi. Idan an sa son zuciya ciki dole ne ya sa a gyara.

Mai taimakawa shugaban kan majalisar wakilai Kawu Simaila yace shugaban zai duba kasafin a tsanake saboda daukan matakin da ya dace. Yace ministoci ma suna dubawa kana su shaidawa shugaban abubuwan da suka gano.

Yanzu dai sai shugaban ya dawo daga ziyar zuwa kasar China za'a sanar da duniya yadda ta kwana.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG