Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Zai Fara Ziyarar Aiki A Kasar Equatorial Guinea


Shugaba Mohammadu Buhari

A yau Litinin ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai fara ziyarar aiki a kasar Equatorial Guinea, makasudin ziyarar kuwa shine hadin kai da makwabtan Najeriya domin a sami hanyar magance matsalar tsaro da ta damu kasar.

Shugaba Buhari dai yace yana son ya fuskanci matsalar Boko Haram, a Arewa maso Gabashin kasar inda yace idan yayi maganin ta, to zai mayar da hankali zuwa Kudu maso Kudu domin kawo karshen satar gurbataccen Man fetur da fashi da akeyi akan jiragen ruwa, da shigo da makamai don yin ta’addanci.

Kakakin fadar shugaban kasar Najeriya, Mallam Garba Shehu, yace wannan ziyara ci gaba ne akan ziyarar da yake kaiwa ga makwabtan Najeriya.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Dakta Aliyu Idi Hong, yace wannan ziyara na da muhimmanci ga tarayyar Najeriya. Shima hafsan sojan Najeriya mai murabus Aliko El-Rasheed Haroon, na kallon wannan ziyara ne ta fuskar tsaro.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG