Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta bada goyon bayan kariyar kamfanonin sarrafa rigakafin COVID-19, a taron Hukumar Kasuwanci ta Duniya.


White House
White House

Wakiliyar harkokin kasuwancin Amurka, Jakada Katherine Tai ce ta sanar da manufofin gwamantin Biden. "Wannan matsalar lafiya ta duniya ce, kuma wannan yanayi da ba’a taba ganin irinsa ba na cutar COVID-19 na bukatar daukan matakai na musamman da ba’a taba irinsa ba," ta rubuta a cikin wata sanarwa. "Gwamnatin ta yi imani sosai na kare ‘yancin mallaka ga duk masu samar da shi,sai dai a yunkurin aikin shawo kan wannan annoba, tana kuma goyon bayan janye wannan kariyar ‘yancin mallakar sarrafa alluran rigakafin COVID-19."

A cikin bayanin nata, Jakada Tai ta ce Amurka “za ta tsoma kanta cikin tattaunawar a Kungiyar Ciniki ta Duniya. Wannan tattaunawar za ta dauki lokaci mai tsawo ganin irin tsarin cibiyar da kuma sarkakiyar batutuwan.

Yawancin ƙasashe masu tasowa ba su da damar samun maganin rigakafin COVID-19 kuma suna ta ƙoƙari don ganin sun hana yaduwar COVID-19 din tsakanin al’ummarsu. Darakta-Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi maraba da shawarar ta Amurka, yana mai kiranta "wani babban cigaba" kuma wani "misali mai karfi na shugabancin Amurka don magance matsalolin kiwon lafiyar duniya."

Jakada Tai ta ce, “Manufar gwamanatin ita ce samar da allurar rigakafi masu inganci ga mutane da yawa cikin sauri. Yayin da aka samar da allurar rigakafinmu ga jama'ar Amurka, Gwamnatin za ta ci gaba da haɓaka ƙoƙarinta - aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu da duk abokan hulɗa - don faɗaɗa masana'antar rigakafi da rarrabawa. Kuma hakan zai yi aiki don kara kayan da ake bukata don samar da wadannan alluran. ”

XS
SM
MD
LG