Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Na Amurka Yace Za Ayi Wa Aikin Gwamnati Kwaskwarima.


GOP 2016 Convention

Shugaba Donald Trump yace ba makawa sai anyi wa tsarin ayyukan gwamnati kwaskwarima,Ga bisa dukkan alamu yana shagube ne ga sakataren lafiya Tom Price.

Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda yace ya zo ya yi wa harakar aikin gwamnati “wankan tsarki”, bisa ga alama yana fushi da akalla daya daga cikin ministocinsa da ake zargin yana almubazzaranci da mankudan kudade wajen shawagin da yake yi da jiragen sama.

Wanda Trump ke hararan kuwa ba wani bane illa Sakataren lafiya na Amurka, Tom Price wanda, da ‘yanjaridu suka tambayi Trump ko zai kore shi, sai yace “zamu dai gani.”

Amma dai Trump ya fito fili yace bai ji dadin rahottanin da aka bada ba na yadda Price, akalla sau biyu, yayi hayar jiragen tafi-da-gidanka maimakon ya shiga jiragen kasuwa, hayar da akace ta janyowa muitanen Amurka asarar $400,000.

A jiya ne Kwamitin Maida hankalin Kan Kashe Kudaden Gwamnati na Majalisar Wakilan Amurka ya aika wasiku zuwa ga fadar ta White House da wasu ma’aikatu, yana neman bayani akan kusoshin gwamnati masu yawan atfiye-tafiye a cikin jiragen haya don gudanarda aiyukkansu ko don ganin damarsu.

Shi wannan sakataren lafiyar Price da ake zance a kansa a yanzu, ya taba sukar lamirin jagabar ‘yanmajalisar jam’iyyar Democrats, Nancy Pelosi a shekarar 2010, akan cewa wai ta cika anfani da jiragen tafi-da-gidanka wajen yawace-yawace.

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG