Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Hugo Chavez Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasa


Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez

Jami’an hukumar zaben kasar Venezuela sun bayyana cewar shugaba Hugo Chavez ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya lahadi. Abokin takararsa Henrique Capriles tuni har yaje ya yiwa Chavez murna.

Jiya lahadi, al’ummar kasar Venezuela, suka je rumfunan zaben shugaban kasar da ake ganin yafi kowane muhimmanci ganin yadda shugaba mai ra’ayin rikau Hugo Chavez ke fuskantar kalubale mai karfin da bai taba haduwa da shi ba cikin shekaru goma sha hudun da yayi yana mulki.

Kafin zaben na jiya lahadi, kididdigar jin ra’ayin masu jefa kuri’a na yin nuni da cewar, tana yiwuwa shugaba Chavez ya sake samun nasara ko kuma ayi kunnen doki tsakaninsa da abokin takararsa Henrique Capriles.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG