Shugaba Goodluck Jonathan, ya amince da tsayarda shi da jamiyarsu ta PDP, tayi, na tsayawa takara a zaben badi, koda yake, shugaba Jonathan, ne dan takara daya tilo, wakilan jamiyar, daga dukan jihohin Najeriya, su dubu biyu da dari takwas da goma sha biyu, sun kadawa Jonathan, kuri’unsu kuma ba ko kuri’a daya a cewar shugaban zaben Ken Nnamani da tayi batan kai.
Shugaba Jonathan, ya kawar da rade-radin da ake yi cewa zai jinginar da mataimakinsa, Namadi Sambo, a sabuwar takarar, inda yace shi zai sake yi masa mataimaki, da bayana shi da kuma cewa mai matukar biyayya ne.
Shugaban wanda yace zai ci gaba da yakar ta’addanci, da nuna cewa tun yakin basasa, Najeriya, bata fuskanci kalubalen tsaro kamar yanzu ba, zai dai shugaban, a wannan karon bai ambaci sunan Boko Haram, ko so daya ba a tsawon jawabinsa na fiye da minti talatin, da ya karanta da taimakon , wasu manyan allunan karanta sakoni na nau’ra mai kwakwalwa, haka jawabin bai tabo sabbin boma-bomai, da suka fashe, a Kano ba.