Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Yaba da Irin Manya da Jihar Niger ta Baiwa Najeriya


Hoton Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan.

A Ci gaba da yakin neman zabe, Shugaba Jonathan, Talata ya ziyarci jihar Niger.

Da yaka jawabi tunda farko mai masaukin baki, Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Neja yayi shagube ne ga wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP. Yana cewa shi karkashin inuwar PDP aka zabe shi, da sauya sheka, da tuni yayi murabus.

Shi kuma a nasa jawabin, Shugaba Goodluck Jonathan yayi magana ne kan irin mashahuran mutane da asalinsu daga jihar Neja. Mr. Jonathan yace tsohon shugaban Najeriya na farko mashahurin dan Afirka Dr. Namdi Azikwe, da tsohon dan tawaye Odumegu Ojukwu, da Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da Janar Abdulsalami Abubakar duk an haifesu a jihar Neja.

Shugaba Jonathan wanda ya ziyarci tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma sarkin Minna Alhaji Umar Farouk Bahago.

Sai dai shugaban kasar bai yi magana kan matsalolin tsaro da kasar take fuskanta ba.

Ga rahoto.

Shugaba Jonathan Yaje Jihar Neja - 2'54"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG