Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Kagame Na Rwanda Ya Lashe Zaben Kasar Da Aka Yi Ranar Jumma'a.


Paul Kagame, lokacinda yake jefa kuri'arsa.

Hukumar zaben kasar tace shugaba kagame ya sami kashi 98 cikin dari na kuri'u da aka kada.

A Rwanda, hukumar zaben kasar tace shugaba Paul Kagame ya sami nasarar wa'adi na uku bayan da ya lashe zaben kasar da gagarumar rinjaye.

Hukumar ta ce kwariya-kwariyar sakamakon zaben da aka gudanar jiya jumma'a, ya nuna cewa shugaban ya sami kashi 98 cikin dari. A wani gangamin yakin neman zabe cikin watan Yuli, shugaba Kagame ya gayawa magoya bayansa cewa "ranar zabe rana ce da za'a tabbatar da abunda aka riga aka sani."

A jawabinsa shugaba Kagame yace "wannan wasu shekaru bakwai nedomin domin tunkarar matsaloli da suka dami 'yan Rwanda, kuma tabbatar da cewa mun kasance cikakkun 'yan Rwanda wadanda suke samun ci gaban tattalin arziki.
Abokanan hamayyarsa sune Frank Habineza na jam'iyyar Green party, da kuma dan Indipenda Philippe Mpayimana.

Shakaru 17 kenan Kagame yake mulkin kasar. Wata kuri'ar raba gardama kan kwaskwarima ga tsarin mulkin kasar da aka yi a 2015 wanda kashi 98 cikin dari na jama'a suka amince da shi, zai baiwa shugaba Kagame damar ci gaba da mulki kasar har zuwa shekara ta 2034.

Ana aza nasarar daidaita kasar bayan kisan kare dangi da aka yi a 1994 kan shugabancin Kagame.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG