Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Kim Ya Gargadi Amurka Kan Takunkumanta

Trump Kim Summit
Trump Kim Summit

A wannan makon ne shugaba Trump ya ce, yana duba yiwuwar sake wani zama da Kim, amma ya jaddada cewa, Amurka ba za ta sassauta takunkumin da ta sakawa Korea ta Arewan ba, har sai ta lalata makamanta na nukiliya.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya ce zai bai wa Amurka wa’adin nan da zuwa karshen shekarar nan, domin ta dauki kwakkwarar matsaya kan tattaunawar da suke yi game da batun nukiliyanta.

Kim ya yi gargadin cewa, za a iya fuskantar mummunan sakamako, muddin hukumomi a Washington, ba su sauya yadda suke tafiyar da wannan al’amari ba.

Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, wacce ake mata kallon ta jeka-na-yi-ka ce, shugaba Kim, ya ce a shirye yake ya kara wata tattaunawa ta uku da takwaran aikinsa Donald Trump, amma har sai Amurka ta sauya irin halayarr da take nunawa, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta Korea ta Arewa ta bayyana.

A wannan makon ne shugaba Trump ya ce, yana duba yiwuwar sake wani zama da Kim, amma ya jaddada cewa, Amurka ba za ta sassauta takunkumin da ta sakawa Korea ta Arewan ba, har sai ta lalata makamanta na nukiliya.

“Muna so takunkuman su ci gaba da kasancewa, a irin tawa fahimtar, ba mu nuna matsi sosai ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG