Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Mugabe Ba Shi Da Niyyar Sauka Daga Mulki


Shugaban Zimbabwe wanda ya dade yana mulki kasar Robert Mugabe, ya yi kunen kashi ga wa'adin da aka bashi zuwa karfe 12:00 na ranar litinin da yayi murabus ko a tsige shi. Mugabe a wani jawabin da ya yi ta telebishan ranar Lahadi, ya ce ba shi da niyan sauka daga mulki.

Miliyoyin 'yan kasar ne saurari jawabin ta radiyoyin su da telebijin da tsamanin cewa za su yi bikin ganin mulkin kama-karya na shekaru 37 karkashin Mugabe.

Sun yi matukar bakin ciki inda wasu daga ciki har zubda hawaye suka yi, yada suka ji mugabe na ikirarin zai shugabanci babban taron na jami'yar ZANU-PF mai mulkin kasar a wata mai zuwa.

A jawabin nasa Mugabe bai ambaci batun yin murabus, kuma bai nuna alaman cewa ya dauki shigowar da sojoji cikin rikicin siyasar kasar da wani muhimmanci ba.

A taron da jam'iyyar ta ZANU-PF mai mulkin kasar tayi a jiya Lahadi ne ta bashi wa'adin, kuma ta dauki matakin korarsa a zaman shugaban jam'iyar, wacce yana daga cikin wadanda suka kafa ta. Shugabannin jam'iyyar sun nada mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, wanda ya kora a farkon watan nan a zaman sabon shugaban jam'iyyar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG