Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama da Shugaba Putin Sun Gana Kan Syria


Shugaban Amurka Obama da Shugaban Rasha Putin

Shugaban Amurka Barack Obama da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun gana a kebe a birnin New York wurin taron Majalisar Dinkin Duniya

A wani kebabben zama baya ga na taron shugabannin duniya na Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a New York. Shugaban Rasha Vladamir Putin da Obama na Amurka, sun tattauna su biyu game da ra’ayoyinsu akan kasar Syria.

Inda dukansu ba su yarda da rawar da shugaban Syria Bashar Al’assad ke takawa ba. Amma sun amince da kiyaye hanyar junansu ta fuskar karfin soja.

Wani jami’in fadar Amurka ta White House yace, wannan tattaunawar da shugabannin suka yi ta kusan mintuna 90 a New York, ba tana nufin cimma wata yarjejeniya ba ne, sai dai neman hanyar tattauna matsalar Syria.

Amurka dai bata kallon sojoji da kayan yakin Rasha da ke Syria a matsayin na magance matsalar kasa, illa kurum suna kare kadarorin kasar ta Rasha ne.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG