Accessibility links

Shugaba Obama Ya Bayyana Halin Da Kasar Amurka Ke Ciki

  • Grace Alheri Abdu

Kakakin Majalisar Wakilan Amura John Boehner (R-OH) da mataimakin Shugaban kasa (H) stand suna tafi lokacin da shugaba Barack Obama yake jawabi
Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce sojojin Amurka 34,000 zasu dawo Amurka daga Afghanistan a shekara mai zuwa. wanna zai sa Amurka yin hanzari akan kokarinta na maido da dakarun gida a shekara 2014 kamar yadda aka shirya.
Shugaba Obama yace, za a ci gaba da janye dakarun, kuma zuwa karshen shekara mai zuwa, yakin da ake yi a Afghanistan zai zo karshe.

A bayaninsa na shekara-shekara da ya yi a gaban ‘yan majalisar dokokin Amurka, wanda kuma shine karo na na biyu da ya ke gabatar da irinsa a matsayinsa na shugabantar Amurka, Mr. Obama ya riga ya fidda shirin sa na shekara mai zuwa.
Bayan bayanin da ya yi a lokacin da aka rantsar da shi shugaban kasa a watan da ya gabata inda ya jaddada batutuwan zaman takewar rayuwa, Mr. Obama yayi amfani da bayanin halin da kasa take ciki don kara maida hankali akan shirin sa na bunkasa tattalin arzikin Amurka.

Mr. Obama yayi kira ga jam’iyyun biyu da ke majalisa da su bada goyon baya akan shirin da ya ayyana yi don taimakawa masu matsakaicin karfi, samar da ayyukan yi da kuma rage gibin kasafi.

Yace, “Babu abin da na fadi a daren yau da zai kara gibin kasafi koda na kwabo ne, ba wai babbar gwamnati muke bukata ba, amma gwamnati mai amfani wadda za ta tsara shirinta bisaga muhimmanci da kuma sanya jari wuraren da za a sami ci gaba.”

Shugaba Obama ya kuma kara da cewa “abubuwan da ban haushi da suka faru jiya da dare zasu kawo wariya ne kawai, idan muka tsayawa kawayen mu, muka kuma karfafa makaman tsaron mu, mu kuma dauki gabarar jagorantar duniya bisa ga barazanar kawo wa”.

Mr. Obama ya kara da cewa amurka da kawayenta za su yi abin da ya dace don su hana Iran samun mukaman nukiliya.

Akan Syria kuma, shugaban ya yi alkawarin kara hura wa gwamnatin wuta, amma bai ambaci sa hannu sojoji ba.

Shi dai wannan jawabin na “halin da kasa ke ciki” an tanade shi ne a cikin kundin tsarin mulkin Amurka inda aka nemi shugaban kasa ya rinka bayyana sau daya kowace shekara a gaban majalisar dokoki don yi wa ‘yan kasa bayanin halin da kasa ke ciki.
XS
SM
MD
LG