Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya Nemi Amincewar Majalisa Don Amfani da Karfin Soji Akan Mayakan ISIL.


Shugaba Barack Obama lokacin da yake jawabin shekara shekara
Shugaba Barack Obama lokacin da yake jawabin shekara shekara

Shugaba Barack Obama yayi amfani da taron jawabinsa na shekara shekara dake neman majalisar dokokin Amurka ta amince da amfani da karfin soji akan mayakan ISIL.

Da yake jawabi a gaban majalisar dake karkashin jam’iyyar Republican, Mr. Obama ya bayyana cewa kasar Amurka na dakile bunkasar mayakan ISIL a Iraqi da Syria. Sai dai ya kara da cewa yakar kungiyar zai dauki lokaci da nutsuwa.

Shugaban ya kara da cewa kasar Amurka har yanzu tana tare da sauran kasashe dake kawance da ita kut-da-kut, sannan an kebance kasar Rasha kana tattalin arzikinta yana cikin matsala.


Ya kara da cewa yaji wasu mutane suna cewa farmakin shugaban Rasha Vladimir Putin akan Ukraine hikima ce da nuna karfin iko.

Amma shugaban yace Amurka zata cigaba da tallafawa Demokradiyyar Ukraine, da kuma tabbatarwa kasashen NATO cewa za’a cigaba da yunkurin ganin cewa manyan kasashe basu tsangwama wa kanana ba.

Dangane da yankin Asiya da Pacific kuma, Mr. Obama yace kasar Amurka na sabunta kawancenta da kasashen yankin, da kuma tabbatarwa sauran kasashe sunbi dokokin da aka gindaya wajen warware takkadamar iyakoki a cikin teku.

Dangane da Ebola, shugaban yace yana alfahari da Sojojin Amurka, Likitoci, da ma’akatain kiwon lafiya da kwararru dake taimakawa wajen ceto rayuka da dakile yaduwar cutar.

XS
SM
MD
LG