Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya sauka Ayaland Ta Arewa tare da iyalansa


Shugaban Amurka a taron kasashe takwas da suka fi arziki a duniya

Shugaba Obama na Amurka da iyalansa sun sauka birnin Belfast ta Ireland Ta Arewa domin halartar taron kasashe takwas da suka fi arziki a duniya da aka sani da suna G8.

Shugaba Obama na Amurka da iyalansa sun sauka birnin Belfast ta Ireland Ta Arewa domin halartar taron kasashe takwas da suka fi arziki a duniya da aka sani da suna G8.
Dimbin matasan kasar suka hallara domin su yi ma shugaban da iyalansa marhaban.

Lokacin da take gabatar da maigidanta ga matasan Mrs. Michelle Obama ta tabbatar masu cewa bayan rikice-rikicen da Ireland Ta Arewa ta yi fama da shi shekara da shekaru matasa a yanzu suna kan gimshiki mai karfi domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasarsu.

Shugaban da matarsa da 'ya'yansu biyu da suka sauka da asubahi sun samu kyakyawar karba. A cikin jawabinsa ga matasan shugaba Obama ya tabo irin munanan matsayi da Ireland Ta Arewa ta yi ta fama da su. Ya ce har yanzu akwai rauni da basu warke ba. Har yanzu akwai jinsuna dake zaman dar-dar domin basu yarda da juna ba.Har yanzu akwai shingaye da suka raba al'umma. Har yanzu akwai tafiya ta milamilai a gabanmu. Ya ce tun da farko muna sane cewa tafarkin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tafarki ne mai nisan gaske. Don haka, inji Obama wannan lokaci ne da zamu tashi cikin gaggawa mu nemi zaman lafiya mai dorewa.

Wakilinmu Sani Dauda nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG