Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya yi watsi da gina bututun mai tsakanin Canada da Amirka


Keystone Pipeline
Keystone Pipeline

Bayan anyi shekaru bakwai ana yin muhawara, jiya juma'a shugaba Barack Obama na Amirka yayi watsi da gina bututun mai na Keyston da ake ta cacar baki akai, da ake son ginawa daga jihohin da ake hako mai a kasar Canada zuwan yankin tsakiyar Amirka.

Bayan anyi shekaru bakwai ana yin muhawara, jiya juma'a shugaba Barack Obama na Amirka yayi watsi da gina bututun mai na Keyston da ake ta cacar baki akai, da ake son ginawa daga jihohin da ake hako mai a kasar Canada zuwan yankin tsakiyar Amirka.
Shugaba Obama ya fada a fadar Whote House cewa bututun mai mai tsawon kilomita dubu daya da dari tara, ba zai biya bukatun Amirka ba.
Haka kuma yace bututun mai ba zai bada gudumawa ga bunkasar tattalin arzikin Amirka na lokaci mai tsawo ba, ta hanyar samar da aiyukan yi ko kuma rage farashin mai wa mutanen da suka mallaki motoci anan Amirka. Shugaba Obama yace tuni ya bugawa sabon Prime Ministan Canada Justin Trudeau ya baiyana masa shawarar daya yanke gameda bututun.
Dama kuwa masu hankoron kare yanayi sun dade suna ikirarin cewa shirin na Keystone zai kara gurbata yanayi. An shirya gina bututun man ne domin jigilar garwan danyen mai dubu dari takwas a kullu yaumin daga Canada zuwa madatsun mai a jihar Texas nan Amirka.
Shugaba Obama yace Amirka ita ke jagorancin rage yawan hayaki masu gurbace yanayi domin yaki da canjin yanayi, a saboda haka ta amince a gina bututun man, zai dagula matsayin duniya kafin taron da za'a yi akan yanayi a watan gobe idan Allah ya kaimu a birnin Paris na kasar Faransa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG