Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya ci gaba da kare yarjejeniyar nukiliya da Iran

Shugaba Barack Obama na Amurka
Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaba Barack Obama na Amirka yace yarjejeniyar da aka kula da Iran akan shirin nukiliyarta zata toshe mata duk wata kafar da take da shi na kera bam din atam. Shugaba Obama yayi wannan furucin ne a lokacinda yake maida martani ga damuwar da Yahudawan Amirka suka nuna akan yarjejeniyar.

Mr Obama ya bada gudumawa ga wani shirin da wasu kungiyoyin Yahudawa suka shirya ta gidan talibiji na yanar gizo da suka yi shiri makamancin wannan da Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da sakataren makamashin Amirka Ernest Moniz.
Shugaba Obama yace sunyi watani suna tattaunawa da gwamnati Isira'ila akan yadda zasu inganta hadin kai ta fuskar matakan tsaro da inganta musayar bayanan sirri da kuma yadda zasu dakile tasirin Iran a yankin.
Ita dai gwamnatin Isira'ila bata goyon bayan yarjejeniyar da zata hana Iran kera bam din nukiliya domin a sausauta mata takunkunmin da kasashen yammacin duniya da Amirka suka aza mata.
Mr Obama yace kodayake yarjejeniyar ba zata magance dukkan matsalolin su da Iran ba to amma yafi babu mafilace da bakin da. Yace sun san cewa gwamnatin Isira'ila ta san da haka.
Haka kuma yace babu wani bangare na yarjejeniyar da zai hannu su ci gaba da matsa lambar dakile aiyukan ta'adanci

XS
SM
MD
LG